Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Bait (As) - ABNA - ya habarta cewa: Yisrael Kats ya rubuta a cikin shafin sada zumunta na dandalin "X" cewa: Za mu yi aiki tare don cin nasara kan abokan gaba da kuma cimma burin yakin.
Kats ya ci gaba rubuta cewa: Manufofin yakin su ne dawo da dukkan wadanda aka yi garkuwa da su, da share kungiyar Hamas a zirin Gaza, da fatattakar Hizbullah ta kasar Labanon, da dakile ta'addancin Iran, da mayar da mazauna arewa da kudu gidajensu lafiya.